An Kama Su Za Šu Kàiwa 'Ýan Binďiģa Maķamai Daga Jihar Filato Zuwa Jihar Zamfara

Daga tashar mota na garin Barikin-Ladi a jihar Pilato, jami'an tsaro sun kama Firdausi Hassan da Sani Musa Isah sun yi dakon harsashin bindiģa sama da dari biyar za su kai wa barayin daji a jihar Zamfara.

Firdausi da Sani sun bayyana cewa ba wannan karon bane suka fara wannan bakar sana'a, sun kai makamai zuwa Zamfara ya fi a kirga.

Sannan jami'an tsaro sun samu nasara kama Alhaji Adamu Bajara a yankin Pankshin na jihar Filato wanda shi ma yake sana'ar sayar da makamai wa 'yan ta'àďda, shine yake zaune da ankwa a hannunsa.

Iyaye mata an san su da tausayi, a duk lokacin da naga an kama mace a cikin tawagar masu safaran makamai da ake kashe 'yan uwansu da shi, na kan tambayi kaina menene dalilin da yasa mata suka fara shiga wannan muguwar bakar sana'a?

A tunanina idan har yunwa ne ko talauci yake sa mata shiga sana'ar, to har gara mace tayi karuwanci da ta shiga wannan bakar sana'a da ake zubar da jinin bayin Allah da shi, duk da karuwancin shima zunubi ne mai girma.

Daga Datti Assalafiy
Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org