An Kwace Kwangilar Gyaran Titin Abuja-Kaduna.
An Kwace Kwangilar Gyaran Titin Abuja-Kaduna.
Gwamnatin Nijeriya ta ƙwace aikin gyaran Titin Abuja zuwa Kaduna daga hannun kamfanin Julius Berger.
Ina za a iya tunawa, a shekarar 2016 gwamnatin tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ta ba wa kamfanin na Julius Berger aikin gyaran Titin, amma bayan shekaru takwas abin da kamfanin ya kammala zuwa yau bai fi Kashi 27% na aikin ba.
Ministan Ayyuka, David Umahi, ya zargi kamfanin Julius Berger da siyasantar da aikin gyaran titin Abuja zuwa Kaduna, inda Kamfanin ke amfani da hwkan wajen tatsar gwamnatin kasa makudan kuɗaɗe.
Umahi ya bayyana cewar an raba wa kamfanonin Dangote da BUA ɓangaren aikin da aka ƙwace daga Julius Berger domin su ƙarasa shi cikin lokaci.
Umahi ya kara da cewar, kamfanonin BUA da Dangote za su gina titin kankare ne, kuma za a biya su ne daga shirin gwamnati na zamiyar kuɗaɗen haraji.