Ana shirin samar da Kudirin Doka da zai zama tilas sai anyi gwajin Genotype ga ma'aurata.
Majalisar Wakilai ta Najeriya ta gabatar da kudirin doka mai suna "Kudirin Duba cutar Genotype Zuwa ga ma'aurata Tilas, 2024" don karantawa a karon farko.
Wannan kudiri yana da nufin tilasta gwajin genotype ga ‘yan Najeriya domin rage yawaitar matsalolin lafiya da ake samu bayan Anyi Aure.
Don tabbatar da kwayoyin halitta kamar su sikila (sickle cell anaemia).da sauransu.
Dan majalisa Hon. Akintunde Rotimi daga jihar Ekiti, wanda yake mai magana da yawun majalisa, ne ya dauki nauyin wannan kudiri. Hon. Rotimi ya yi bayani cewa manufar kudirin ita ce taimakawa wajen kare lafiyar al’umma da kuma kawar da damuwar cututtuka masu alaka da halayen jini a cikin iyalai.
Manufar Kudirin Doka: Wannan kudiri na bukatar dukkan 'yan Najeriya su gudanar da gwajin genotype a matsayin wajibi, musamman ma masu shirin yin aure.
Idan aka aiwatar da wannan doka, za a tabbatar da cewa dukkan mutane sun san irin kwayar jini da suke dauke da ita domin samun kariya daga matsalolin cututtuka na kwayoyin halitta.
Idan aka aiwatar da wannan kudiri, ana sa ran zai taimaka wajen rage yawan matsalolin da cutar sikila ke haifarwa, musamman ga ma’aurata da yara.
Hakan zai kuma rage nauyin da ake samu a asibitoci da kuma kara karfin lafiyar al’umma baki daya.
Kammalawa: Kudirin doka na Duba Genotype Zuwaga Tilas, 2024, wanda Hon. Akintunde Rotimi ya dauki nauyin gabatarwa, yana da mahimmanci wajen tabbatar da lafiyar al’umma da kuma rage yawaitar cututtukan da ke da alaka da kwayoyin halitta. Ana sa ran majalisar za ta ci gaba da nazari a kansa domin tabbatar da dacewar wannan kudiri ga al’ummar Najeriya.