Arteta ya bayyana dalilin da yasa Arsenal ta sha kashi a hannun Bournemouth da ci 2-0

Kocin Arsenal Mikel Arteta ya ce jan katin da aka bai wa William Saliba ya dagula masu lissafi, kuma sun tabbatar da cewa ba ƙaramin aiki bane doke Bournemouth a wannan yanayin.

Gunners ta yi rashin nasara da ci 2-0 a hannun Bournemouth bayan jan katin da aka basu a rabin farko na fafata wasan.

An bai wa Saliba jan kati ne sakamakon ƙeta da yayi a matsayin sa na ɗan wasan ƙarshe a baya bayan da Leandro Trossard ya bashi ƙwallo ba yadda ya dace ba.

Ryan Christie da Justin Kluivert ne suka zura kwallayen a ragar Arsenal bayan dawowa hutun rabin lokaci.

Da yake magana bayan wasan, Arteta ya ce: "Tabbas mun ji takaici da sakamakon kuma mun yi fargaba saboda dole ne mu buga wasa na tsawon minti 60 zuwa 65 da ƴan wasa 10, wanda hakan abu ne mai wuya ace mun yi nasara.

Dangane da jan katin, ya ƙara da cewa: “An riga da an yanke shawara a filin wasa. Don haka ba za mu ce komai ba, mun ɗauka, domin an riga an yanke hukunci.

"Saliba bai taba yin irin wannan ba, kuma bai yi hakan da gangan ba. Sannan hakan na faruwa ga ƴan wasa, don haka dole ne mu yi masa uzuri, a tari gaba, za mu huce haushin mu a ranar Talata idan maka haɗu da kungiyar Shakhtar Donestsk" Inji Arteta.

Daga Lukman Aliyu Iyatawa
Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org