BATUN GASKIYA BA MU SAN LOKACIN DA ZAMU GAMA GYARAN WUTA BA; TCN

Shuaibu Abdullahi 

Rahotan babbar ma'aikatar Samar da Wutar Lantarki na kasa TCN ya ce za a ci gaba da fuskantar matsalar wutar lantarki da ake fama da shi a wasu daga cikin jihohin kasar nan Yan Kwanakin nan, sakamakon ƙalubalen tsaro da ke kawo cikas wajen aikin gyara layukan wutar da suka sami matsala.

Shugabar kamfanin ta TCN Nafisatu Asabe Ali ta bayyana cewa ba za a iya cewa ga takamaiman lokacin da za a gyara layin wutar da ya samu matsala ba saboda matsalar tsaro.

Asabe, ta ce sun dade da samar da dukkanin kayayyakin da ake bukata saboda gyaran to amma barazanar tsaro bazata bari ayi gaggawar kammala aikin ba har sai sun sami tabbaci. 

Kusan mako guda kenan da layin Wutar ta sami matsala daga Shiroro zuwa samar lantarki ta Mando dake gundumar Afaka a karamar hukumar Igabi ta Jihar Kaduna.

Lamuran kasuwanci yaja baya sosai wasu ma da dama sun tafka asarar miliyoyin kudade saboda wannan matsalar, Kuma matsalar ta shafin hukumar samar da wuta sosai saboda rashin Siyan Katin Wuta da Kuma shakka zuwa karbo kudin wuta saboda rashin ta, Wanda ke barazana da Kafar samar da kudaden shigar biyan albashi da sauran lamuran kamfanin samar da Wutar Lantarki Mai zaman Kai.
Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org