DA DUMI-DUMI: Shugaba Tinubu Yayi wa Gwamnatinsa Gyaran Fuska
Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin haɗe wasu ma'aikatu da wasu hukumomin gwamnati wuri daya Kana ya ƙirƙiru wasu.
Wata sanarwa da mai magana da yawun fadar shugaban kasar ya fitar ta ce, shugaban ya ba da umarnin rusa hukumar bunƙasa yankin Neja-Delta da kuma ma'aikatar wasanni.
Bayo Onanuga ya ce a madadin haka, yanzu za a ƙirƙiri ma'aikatar bunƙasa yankuna da za ta kula da hukumomin yankunan da ake da su.
Sai kuma hukumar kula da wasanni ta ƙasa da za ta maye gurbin ma'aikatar wasanni.
Haka nan, majalisar zartarwa ta amince da haɗe ma'aikatar al'adu da ma'aikatar yawon buɗe ido wuri guda....