Dalilin da yasa Shugabanni da Gwamnoni ke gujewa miƙa Mulki ga Mataimakan su – Osoba

A ranar Talata ne tsohon Gwamnan Jihar Ogun, Olusegun Osoba, ya bayyana cewa zargin bita da ƙulli, da rashin yadda ne ya sa da yawa daga cikin shugabanni da Gwamnoni ke kaucewa mika mulki ga mataimakansu.
Dalilin da yasa Shugabanni da Gwamnoni ke gujewa miƙa Mulki ga Mataimakan su – Osoba

Shahararren dan jaridan ya bayyana wadannan dalilan ne a wajen taron shekara shekara na kungiyar tsofaffin Mataimakan Gwamnonin Najeriya karo na uku da aka gudanar a Abuja.


Taron mai taken “Dabarun Samar da shugabanci nagari, Samar da Abinci da kuma Ci gaba mai ɗorewa a Najeriya,” ya yi nuni da irin waɗannan ƙalubalen da ake fuskanta na shugabanci.

Yayin da yake bayyana lamarin a matsayin abin takaici, Osoba ya ce, batu ne da ya shafi duniya baki daya, ba wai kawai iya Najeriya ko Afirka ba.

Tsohon Gwamnan ya buga misali da rikicin siyasar da ke tsakanin tsohon Mataimakin Shugaban ƙasar Amurka Al Gore da shugabansa Bill Clinton.

Ya ce, “Abin takaici ne. ba wai iya a Afirka bane hakan ke faruwa - yana faruwa a duka duniya. Za ku tuna al'amarin Al Gore da Bill Clinton. Al Gore shi ne mataimakinsa, kuma ya tsaya takarar shugaban kasa. Amma saboda yana ganin Clinton na iya zama masa Matsala bai sa shi cikin kwamitin yaƙin neman zaɓen sa ba.

“Don haka, wannan batu bai takaitu ga Nijeriya ba. Yana da wuya ka ga mataimaki ya gaji maigidansa a shugabanci. Sai dai har yanzu akwai damammaki ga Matasan kasar nan.

Osoba ya kuma koka da yadda gwamnoni ke ƙulla makarkashiya ko daukar nauyin tsige mataimakansu.

Da aka tambaye shi ko za a iya gyara kundin tsarin mulkin kasar domin bada kariya Mataimaka daga Shugansu a gwamnati, dan siyasar ya ce babu wani abu da za a iya yi sai dai suyi kokari inganta alaƙa tsakaninsu.

Daga Lukman Aliyu Iyatawa
Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org