Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya "CNG" Ta Gana Da Gwamnatin Tarayya Don Karɓar Shawarwarin Kwamitin Tsaro Na CNG.
A ci gaba da kokarin da Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya (CNG) ke yi na samun mafita mai dorewa ga matsalolin rashin tsaro dake addabar arewacin Najeriya, an shirya wani muhimmin taro a yau a Abuja.
A taron, akwai Mai Baiwa Shugaban Kasa Shawara kan harkokin Tsaro, Mallam Nuhu Ribadu, Babban Ministan Tsaron Najeriya, Muhammad Badaru Abubakar, gwamnonin jihohi biyu da matsalar tsaro tafi shafar jihohinsu da matsalar 'yan fashin daji ya fi shafa, wato Dauda Lawal Dare na Jihar Zamfara da Dikko Umar Radda na Jihar Katsina.
MATSALAR TSARO:- Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriya "CNG" Ta Gana Da Gwamnatin Tarayya Don Karɓar Shawarwarin Kwamitin Tsaro Na CNG.
Gamayyar Kungiyoyin Arewacin Najeriyar ta samu wakilcin Shugaban Kwamitin Amintattu, DR. Nastura Ashiru Shariff; Alhaji Bashir Yusuf, wanda shi ne shugaban Kwamitin Tsaro na CNG, Alhaji Ibrahim Katsina, Janar Sarkin Yaki Bello, Jakada Buhari Bala, da Janar Sa'ad Abubakar.
Wannan taro ya amince da shawarwarin Taron Tsaro da Gamayyar Kungiyoyin Arewa ta shirya a farkon wannan shekara a Abuja, wanda manyan masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na arewacin Najeriya suka halarta.
Muhimmin abinda aka fahimta daga taron yau shi ne shirye-shiryen Gwamnatin Tarayya, gwamnonin jihohi, hukumomin tsaro, da jama'a baki ɗaya don aiki tare wajen samo mafita mai dorewa ga matsalar rashin tsaro.
Yana da muhimmanci a jaddada cewa taron yau ya nuna shirye-shiryen gwamnatoci a matakai daban-daban, tare da CNG, don fara aiwatar da waɗannan shawarwarin nan take, wanda ake fatan zai kawo gagarumin sauyi wajen rage matsalolin tsaro a duk yankunan da suka shiga cikin mawuyacin hali.
Karɓar waɗannan shawarwarin babban mataki ne dake nuna hanyar magance matsalolin tsaro da ake fuskanta a fannoni daban-daban a arewacin Najeriya.