Gwamnonin jihohin arewacin Najeriya sun ce sun ɗauki matakan bai-ɗaya na magance matsalolin da suka addabi yankin.

Gwamnonin jihohin arewacin Najeriya sun ce sun ɗauki matakan bai-ɗaya na magance matsalolin da suka addabi yankin.


Gwamnonin sun ce sun cimma matsaya a taron da suka gudanar a Kaduna, kan yadda za su tunkari matsalolin tsaro da tattalin arziki da suka addabi yankin da matsalar lantarki da ake fuskanta da kuma daukar matakan magance su.

Gwamnan jihar Yobe, Maimala Buni, ya ce suna daukar matakan gaggawa na magance matsalolin da suka addabi arewa da suka hada da matsalar wutar lantarki da kuma matsalar tsaro da ta addabi yankin.

Gwamnan ya ce ba za su sauke wa gwamnatin tarayya nauyin da ke kanta ba saboda akwai haƙƙoƙin arewa a kan ta , "dole mu hada duka domin mu inganta wutar lantarki.

Maimala Buni ya musanta zargi da wasu ke yi na cewa babu haɗin kai tsakanin gwamnaonin arewacin Najeriya, "Akwai haɗin kai sai dai kwai maganar da muka yi ita ce ta yin abu bai ɗaya, tunda matsalolin duk iri ɗaya ne."

"Me za a yi wanda zai zaburar da arewa, musaman kan tatalin arzƙi da tsaro , ilimi da noma, dukkan jihohin arewa musamman arewa maso gabas da arewa maso yamma, ind amatsalolin tsaro suka gawurta."

Gwamnan ya ce hadin kai ne ya sanya suke da shugaba, gwamnan Gombe, Inuwa Yahya, wanda dukkan gwamnonin arewa suka yi masa mubaya'a.

Maimala ya ce taron da gwamnonin suka yi a ranar Litinin a Kaduna ba taron shan shayi bane za su tabbatar sun bibiyi batutuwan da aka tattauna, "Al'umma su yi haƙuri kuma ayi addu'a a ƙasa."

Ƙungiyar Gwamnonin Arewa ta nemi gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi gaggawar shawo kan matsalar wutar lantarki da ake fama da ita a mafi yawan yankin.

Ƙungiyar ta yi kiran ne yayin taron da ta gudanar a ranar Litinin ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya a jihar Kaduna domin tattauna matsalolin da suka dabaibaye yankin.

An shiga mako na biyu da jefa yankunan arewa maso yamma, da arewa maso gabas, da wani ɓangare na arewa ta tsakiyar Najeriya cikin duhu sakamakon abin da hukumomi suka ce aikin "maɓarnata ne".

"Ƙungiyar na kira ga gwamnatin tarayya da hukumomin da suka dace da su gaggauta shawo kan matsalar lantarki da mafi yawan jihohin arewaci ke ciki saboda masu ɓarnata layukan wutar," a cewar wata sanarwar bayan taro da suka fitar.

BBC HAUSA


Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org