Kiran Gaggawa ga Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa PhD
Iyaye da ɗalibai da masu ruwa da tsaki na kira ga mai girma gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa da ya duba batun rufe makarantun kiwon lafiya masu zaman kansu da aka rufe a fadin jihar Katsina domin kauracewa yin asara ga dalibai
Wannan kiran na zuwa ne a daidai lokacin da wasu daga cikin daliban ke fuskantar jarabawar karshe da ake kira National Examination wanda kuma wasu hukumomi ne ke shirya ta matakin ƙasa ba jiha ba
Yanzu haka dai waɗannan makarantu na kiwon lafiya masu zaman kansu suna tunkarar jarabawa da ake shiryawa dalibai matakin ƙasa da ake kira National Examination
Sai dai kuma waɗannan makarantu rufe suke bisa umarnin mai girma gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa har sai an kammala aikin tantance su domin fitar da wadanda ba su cika ka'ida ba.
Saboda wancan Jarabawa ta ƙasa da za a gudanar a ranar labara anan jihar Katsina ake jan hankalin gwamnatin da ta duba wannan batu mai matukar muhimmancin gaske ta yadda za a iya taimakon ɗaliban ba tare da sun shiga wani hali ba.
Ana sa ran cewa za a fara wannan jarabawa a ranar 30/10/2024 wanda hakan tasa ake kira ga mai girma gwamna Malam Dikko Umar Raɗɗa da ya taimaki waɗannan daliban ya ba su damar rubuta wannan Jarabawa ta ƙarshe domin gudun kadda su yi asarar makudan Kuɗaɗan da suka kashe da kuma ɓata wata shekara ɗaya
Kamar yadda wasu iyayen ɗaliban suka bayyana ba suna ƙalubalantar rufe makarantun bane, a'a suna rokon mai girma gwamna da ya duba wannan hali da suke ciki musamman ganin cewa ga lokaci yana kurewa na ita wannan jarabawa ta National Examination.
Suna masu cewa barin daliban su zauna wancan jarabawar zai taimaka matuƙa gaya wajen ganin duk ya biya kuɗin bai yi asarar da sannan bai sake ɓata lokaci ba.
Suma daliban sun yi irin wannan riko inda suka nuna fargaba ga duk dalibin da ke fuskantar wannan jarabawa wanda suka ce idan ta wuce ba a yi hannun agogo ya koma baya
Haka kuma ana rokon ita gwamnatin jihar Katsina da ta duba wannan batun da idon basira ta bada izini ga makarantun kiwon lafiya masu zaman kansu su gudanar da wannan jarabawa.
Kazalika, masu rokon suka ce idan an kammala Jarabawa da za a kwashe kwanaki huɗu kawai ana yin ta, sai a sake rufe makarantun kafin gwamnati ta gama tantancewar da take yi wa makarantun kiwon lafiya masu zaman kansu na jihar Katsina.
Hakika bada wannan dama ta zauna jarabawa ga daliban makarantu kiwon lafiya masu zaman kansu ba karamin taimako gwamantin jihar Katsina zata yi wajen ganin ta karfafa gwiwar iyaye da kuma daliban wajen cigaba da karatun kiwon lafiya a jihar Katsina