Majalisar Dattawa ta nemi a ɗaure iyayen da suka ƙi sanya ƴaƴansu Makaranta
Majalisar dattawan Najeriya ta ce tana son yi wa kundin tsarin Mulkin ƙasar nan kwaskwarima, ta yadda za a samar da dokar hukuncin ɗauri ga iyayen da suka ƙi sanya ƴaƴansu a Makaranta.
Shugaban kwamitin ilimi na Majalisar, Sanata Lawan Adamu Usman ya ce majalisar na duba yiwuwar sanya hukunci ɗauri na tsawon wata shida ga duk iyayen da suka kasa sanya 'ya'yansa a makaranta bayan an yiwa kundin tsarin Mulkin gyaran fuska.
Da yake zantawa da manema labarai, bayan gabatar da rahoton kwamitinsa a gaban majalisar a ranar Laraba, Sanata Lawan ya ce “muna son a yi dokar ɗaurin wata shida ga iyayen da suka ƙi sanya 'ya'yansu a makaranta, yana mai nuni da cewa Ilimi shine mafi muhimmanci a rayuwar ɗan'adam, kuma rashin shi ne babbar matsalar da muke fuskanta a Najeriya.
A Jawabin sa Shugaban Majalisar Dattawan, Sanata Godswill Akpabio ya ce akwai yara fiye da miliyan 20 da ba sa zuwa makaranta a Najeriya, waɗanda ya ce idan ba a ɗauki matakin kula da su ba, za su iya zama ɓata-gari idan suka girma.
Shi ma Mataimakain Shugaban Majalisar, Sanata Barau Jibrin ya ce matsalar rashin zuwan yara makaranta, babbar damuwa ce ga ƙasar, wanda ya ce ta fi ƙamari musamman a yankin Arewacin ƙasar.
Daga Lukman Aliyu Iyatawa