Malaman Addinin Musulunci sun yi jinjina ga Bello Matawalle bisa kisan da aka yi wa rikakken dan bindigar nan Halilu Sububu

Malaman Addinin Musulunci sun yi jinjina ga Bello Matawalle bisa kisan da aka yi wa rikakken dan bindigar nan Halilu Sububu 

Malaman Addinin Musulunci na bangarori daban-daban sun yi yabo da jinjina ga Ministan kasa a ma'aikatar tsaro ta Nijeriya Dr Bello Matawalle bisa ga nasarar da aka samu a baya-bayan nan ta kisan rikakken dan bindigar nan Halilu Sububu da karin wasu 'yan bindiga a yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya.

Shehunan Musuluncin karkashin jagorancin Dr Bashir Aliyu Umar sun yi wannan jinjinar ne a lokacin da suka kai wa Ministan ziyara ta musamman a ofishinsa da ke Abuja.
Dr Bashir Aliyu Umar ya ce hakika nasara ce babba, kakkabe wadannan rikakkun 'yan bindiga cikin kankanin lokaci bayan umurnin da shugaban kasa Bola Tinubu ya ba manyan hafsoshin tsaron Nijeriya na su tare yankin Arewa maso Yammacin kasar har sai sun tabbatar tsaro ya inganta.

A cewarsa, wannan ziyara na da nufin karfafa wa minista Matawalle guiwa tare da jinjina gare shi bisa namijin kokarin da yake yi wajen ganin tsaro ya inganta, ta hanyar komawa Sokoto da zama da ya yi don tabbatar da tsaro ya inganta a yankin.

"A matsayinmu na jagorori a cikin al'umma kuma wakilan al'ummar da muka fito, ya kyautu mu nuna godiyarmu saboda irin nasarorin da aka samu wajen hallaka Halilu Sububu da sauran takwarorinsa da ma yaransa masu tarin yawa".

"Gwamnatin Shugaba Tinubu lallai ta cancanci wannan yabo ita ma, da ta dauki matakin gaggawa don ganin an tsare rayuka da dukiyoyin al'umma."

"Da irin wannan matakin, an cimma nasarori da dama, kuma Alhamdulliah, tsaron na ta inganta idan aka kwatanta da abubuwan da suka faru a baya." In ji Dr Bashir Aliyu Umar.

"Muna addu'a cike da fatar a dore da wadannan matakan da aka dauka ta yadda jagororin 'yan ta'adda irinsu Bello Turji su ma su dandana kudarsu, a samu damar kawar da su don al'umma ta zauna lafiya."

"Alal hakika, muna da kwarin guiwa kan matakan da minista Bello Matawalle da sauran manyan hafsoshin tsaro ke dauka a daidai wannan lokacin da ake tsaka da bukatar wannan mataki. Sannan muna da yakinin cewa cikin hukuncin Allah, za a yi nasarar kawo karshen matsalar tsaro da ta addabi sassan Nijeriya." In ji Dr Bashir.

Malaman na Addinin Musulunci sun kuma yi kira ga 'yan Nijeriya da su cigaba da addu'ar zaman lafiya da ingantuwar tsaro a kasar nan, musamman yankunan da ke fama da kalubalen tsaro.

Sun kuma yi addu'a ga Ministan da sauran manyan hafsoshin tsaron Nijeriya cike fatar Allah Ya ba su nasarar kawo karshen matsalar tsaro a kasar nan.
Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org