Obasanjo: Zan fi son kasancewa dan Najeriya fiye da zama ɗan fafutukar kafa Jamhuriyar Oduduwa

Obasanjo yayi wannan bayanin ne yayin da yake karɓar tawagar ƙungiyar Northern Democrats da tsohon gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya jagoranta a gidansa da ke Abeokuta, Jihar Ogun, ya bayyana tsarin yankin da aka yi amfani da shi kafin samun 'yancin kai a shekarar 1960 a matsayin tushen rashin haɗin kai mai tsawo a ƙasar. 
Ya yi kira da a duba cancanta, ƙwarewa, da iya gudanarwa a matsayin wasu daga cikin abubuwan da ya kamata a yi la'akari da su wajen zaɓen shugabanni ko naɗa wasu mukaman siyasa, maimakon tambayar yankin da mutum ya fito.


Ya ce: “Lokaci ya yi da ya kamata mu fara aiki don cigaban ƙasa. Eh, kun ayyana ƙungiyarku a matsayin League of Northern Democrats amma yayi  daɗi idan za ku kira ƙungiyarku National League of Democrats, domin ba lallai ne daga inda kake ya zama matsala ba.

Inda aka haife ni ba zai zama ƙawancen rashin zama dan Najeriya ba. Zai fi kyau in kasance dan Najeriya fiye da in kasance dan Jamhuriyar Oodua.

“Babu shakka, ina alfahari da kasancewa Bayarbe, amma kasancewata dan Najeriya bai kamata ya zama cikas ga kasancewata Ba yare ba. Dole ne mu sami mafi cancanta domin yin aiki, ba tare da la’akari da yankin da mutum  ya fito ba. Dole ne mu haɗa kai mu yi aiki tare.

“Afirka, bakin fata, da duniya baki ɗaya na kallonmu. Lokacin da muka sami ‘yancin kai, abin da suke kiranmu da shi shi ne babban gunkin rana, amma shin hakan ne halin da ake ciki a yau?

Mun ba kanmu kunya, mun ba wa bakin fata kunya, Afirka da duniya baki ɗaya kunya. Don haka damuwarmu ta dace, mun wargaza kimar gaskiya, babu gaskiya, babu soyayya amma ba muyi latti ba, mu koma kan hanyar da ta dace. Dole ne mu manta da abin da ya gabata mu yi aiki domin kyautata girman Najeriya.”

Game da halin da ƙasar ke ciki, ya nnuna cewa Najeriya a yanzu babu abinda a take bukata sai neman gyara, muddin kowa ya shirya ya haɗa kai ya yi aiki a matsayin ƙasa ɗay

#FTNews

Obasanjo
Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org