Rashin Lantarki a Arewa: Yanzu ina samun abin da zan ciyar da iyalina - Mai Chajin Waya
Wani mai caja wayar salula a unguwar Rogo da ke karamar hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato ya ce rashin wutar lantarki da ake fama da shi a Arewacin Kasar nan ya ƙara haɓaka kasuwancinsa.
Yawancin Jihohin Arewacin Najeriya a halin yanzu suna fama da matsalar rashin wutar lantarki bayan da layukan wutar lantarki mai karfin KV 330 suka katse a Makurdi tsakanin Jihohin Benue da Enugu.
Auwal Bayya, wani mai cajin waya, ya ce, “Rayuwar duniya ta kasance idan wani yana kuka, wani kuma yana dariya”, inda ya yarda cewa matsalar wutar lantarki da ake fama da ita a halin yanzu ta ƙara inganta sana’arsa.
Ya ce, “Rayuwa tana da ɗaci; hawayen wani, dariyar wani ne. Amma gaskiyar magana ita ce, waɗanda ke shan wahala sun fi yawa. Yanzu ina samun isassun kuɗi don ciyar da iyalina, ba kamar a baya ba lokacin da mutane kaɗan ne suke kawo min Chaji.
Amma tun da rashin wutar lantarki ya Kunno kai, mutane na tururuwa a nan don yin cajin wayoyinsu. Ƙarin abokan ciniki yana nufin ƙarin samun kuɗi. Ina cajin wayoyi sama da ɗari kullum, da kwamfyutocin tafi-da-gidanka, fitilu, da sauran kayan lantarki. Wani lokaci, dole in juya wa mutane baya saboda rashin sarari. Kamar yadda kuke gani, ko'ina cike yake da wayoyi".
“Ina daya daga cikin waɗanda ke cin gajiyar lamarin, amma ina tausayawa ƴan Najeriya game da lamarin, sai dai babu abin da zan iya yi. Yanayin ne ya ba da damar haka. Kar ku manta, ni ma ina siyan Man Fetur a farashi mai tsada. Duk abin da na samu, ina rabawa ne tare da masu gidajen Mai, ”in ji shi.
Sai dai Bayya ya buƙaci Gwamnati da hukumomin da abin ya shafa da su maido da wutar lantarki a yankunan da abin ya shafa, duk da cin gajiyar hakan da yake yi.
Ya ce, "Ba za mu iya ci gaba da jin daɗi ba yayin da Miliyoyin mutane ke shan wahala."
Daga Lukman Aliyu Iyatawa