Rikicin Ribas: 'Yan Najeriya suna rasa kwarin Gwiwa kan ɓangaren shari'a – Atiku

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar, ya soki umarnin kotu da ya hana r
CBN Baiwa Jihar Ribas kasonta Na Gwamantin Tarayya.

A Jiya Laraba ne wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta hana Babban Bankin Najeriya (CBN) ci gaba da Baiwa Jihar Ribas kasonta Na Gwamantin Tarayya.

Mai shari’a Joyce Abdulmalik ta yanke hukuncin cewa a dakatar da sakin kuɗaɗe daga asusun tarayya zuwa jihar har sai an gabatar da dokar kasafin kudi daga Majalisar Dokoki da aka kafa bisa ka’ida.

Martins Amaewhule, Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Ribas, ya shigar da wannan kara.

Joyce Abdulmalik ta bayyana cewa gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya yi kuskure wajen gabatar da Kasafin Kudinsa na 2024 ga majalisar dokoki mai mambobi biyar da ba ta cika ka’ida ba.

Atiku, yayin mayar da martani cikin wata sanarwa ta bakin mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, a ranar Laraba, ya yi gargadin cewa matakin bangaren shari’ar na iya “ruruta rikici” a Jihar Ribas.

A cewarsa, abin takaici ne yadda wasu mutane masu biyayya ga gwamnatin tarayya ke amfani da iko daga bayan fage.

Ya tambayi dalilin da ya sa Joyce Abdulmalik ta bayar da umarnin dakatarwa yayin da kalubalen shari’a na Jihar Ribas ke ci gaba a kotun daukaka kara.

“A makon da ya gabata, Kotun Daukaka Kara ta ayyana cewa kasafin kudin Jihar Ribas ba bisa ka’ida ba ne domin an amince da shi ne ta majalisar dokoki da ba ta cika ka’ida ba.

“Kotun ta umarci Gwamna Siminalayi Fubara da ya sake gabatar da kasafin kudin — kuma Gwamnatin Jihar Ribas ta riga ta shigar da kara a Kotun Koli don jin wannan lamari.

“Amma dai wasu mutane a cikin gwamnatin Bola Tinubu sun samu hukuncin da nufin kawar da tasirin Kotun Koli.
Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org