Sai NNPC ta amince kafin mu siyarwa da ƴan Kasuwa Man Fetur – Matatar Dangote

Matatar Man Ɗangote ta ce ba ta samu izini daga Kamfanin Mai na Najeriya NNPC ba na sayar da Man Fetur ga mambobin ƙungiyar dillalan Man Fetur mai zaman kanta ta Najeriya ba.
Ta sanar da hakan ne a ranar Alhamis yayin da dillalan mai a karkashin kungiyar masu sayar da Man Fetur ta Najeriya suka buƙaci matatar da ta bayyana masu farashin ta na Man Fetur, tare da jaddada cewa shirun da ta yi kan wannan lamari shine abinda ya dade bisa wannan yarjejeniya.

A ranar Laraba ne Shugaban ƙungiyar IPMAN na kasa, Abubakar Maigandi, ya ce mambobinsa sun je Matatar mai da ke Lekki amma sun kasa samun Man Fetur tsawon kwanaki hudu.

Maigandi yana mayar da martani ne kan kalaman da Shugaban Rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya yi a ranar Talata, cewa Matatar sa na da sama da lita Miliyan 500 na Man Fetur amma ƴan kasuwa masu zaman kansu ba su zuwa saye.

Maigandi ya ce, “Idan da gaske Matatar tana da lita Miliyan 500, to bai kamata a samu dalilin da ya sa mambobinmu ba za su iya yin lodi ba har tsawon kwanaki huɗu. Mu a shirye muke mu siya Mai kai tsaye idan matatar ta shirya siyar mana, amma a halin yanzu mambobinmu ba za su iya ɗauko Mai ba ko da sun biya kuɗi.”

Daga Lukman Aliyu Iyatawa
Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org