Shawarar mu ga Najeriya game da cire tallafin Man Fetur ya zama dole - IMF
Asusun ba da lamuni na duniya IMF, ya ce yana nan akan bakan sa dangane da shawarwarin da yake baiwa Najeriya game da tsarin hada-hadar kuɗaɗen waje, da cire tallafin Man Fetur, yana mai cewa hakan ya zama wajibi don a samu daidaiton tattalin arzikin kasar.
IMF ta sake jaddada matsayinta kan shawarwarin sauya manufofi ga Najeriya ranar Laraba.
Dimokuradiyya TV ta tuna cewa Daraktan yankin Afirka a IMF, Abebe Selassie, ya yaba da sauye-sauyen tattalin arziki da Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta aiwatar a yayin wani taron manema labarai da aka kammala a taron IMF da Bankin Duniya a birnin Washington DC na ƙasar Amurka.
Selassie ya ce IMF za ta ci gaba da bayar da shawara ga Najeriya na ta zuba kuɗi a fannonin ababen more rayuwa, lafiya, da ilimi; yana mai bayyana cire tallafin Man Fetur a matsayin matakin da zai samar da ingantaccen amfani da dukiyar jama'a.
A cewarsa, matakin zai bude babbar hanyar da tattalin arzikin kasar ke da shi, ta yadda za a samu karin hanyoyin haɓaka shi, har ya samu cigaban da zai yi gogayya da na Manyan kasashen Duniya.
Ya kuma shawarci Gwamnatin Najeriya da ta yi amfani da kuɗaɗen da aka samu daga tallafin Man Fetur da aka cire don tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi a cikin halin kuncin da tattalin arzikin ƙasar ke ciki a yanzu.
Sai dai a ranar 25 ga watan Oktoba, kafafen yada labarai na cikin gida sun bayar da rahoton cewa IMF ta musanta cewa tana da hannu wajen cire tallafin Man Fetur.
Daga Lukman Aliyu Iyatawa