"Shugabancin Bola Tinubu ba alheri ba ne, kuma mulkin soja ya fi na dimokuraɗiyya mahimmanci a Najeriya," in ji Mustapha Inuwa
Daga: Abdulrazak Ahmad Jibia
Tsohon sakataren gwamnatin jihar Katsina kuma daraktan yaƙin neman zaɓen Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP a jihar Katsina, Mustapha Mohammed Inuwa, ya soki salon mulkin shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu, inda ya bayyana cewa ƙasar ta samu ci gaba a mulkin soja fiye da dimokuradiyya. Inuwa ya bayyana rashin ayyukan ci gaba da kuma kasa magance muhimman matsalolin da ke addabar Najeriya.
A wata hira da aka yi da shi kwanan nan a shirin Dimokuraɗiyya na Hikaya TV, Mustapha Inuwa ya yi Allah-wadai da shugabancin Bola Tinubu, inda ya bayyana cewa ƙasar nan ba ta samu ci gaba a gwamnatinsa ba.
Inuwa ya kwatanta tasirin mulkin soja da dimokuraɗiyya, yana mai nuni da cewa wancen mulkin na soja da ya gabata ya fi amfani ƙasashen Afirka saboda yadda yake iya magance matsalolin al'umma cikin gaggawa ba tare da ɓata lokaci ba.
Ya kuma caccaki ƴan siyasar Najeriya kan rashin ba da fifiko kan muhimman ayyukan more rayuwa kamar wutar lantarki, ruwa, makarantu, da asibitoci, lamarin da ke haifar da ƙalubalen da jama’a ke fuskanta.
Inuwa ya koka da yadda ake fama da rashin ci gaba a arewacin Najeriya musamman a fannin ilimi da noma, yana mai alaƙanta rikicin yankin da rashin tsaro da rashin inganta makarantu.
Da yake tsokaci matsalolin tsaro a jihar Katsina, Inuwa ya gabatar da wasu muhimman shawarwari guda uku domin yaƙar matsalolin da suke addabiar yankuna daban-daban na jihar.
Shawarar sa ta farko ta jaddada muhimmancin haɗin kai tsakanin jihar Katsina da yankunan da ke makwabtaka da ita, da kuma neman goyon bayan gwamnatin tarayya domin magance matsalolin tsaro yadda ya kamata.
Shawara Mustapha Inuwa ta biyu ta mayar da hankali ne kan samar da muhimman ayyuka a fannin ilimi da kiwon lafiya, biyan bashi da tallafawa ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya, da aiwatar da tsare-tsare na rage zaman kashe wando a tsakanin matasa maza da mata.
Shawara ta uku ta soki kuɗaɗen da aka ware wa wani sabon aikin titi a jihar Katsina, inda Mustapha Inuwa ya nuna shakku kan wajibcinsa da kuma nuna damuwa kan yadda ake rabon kwangilar gwamnati ba bisa ƙa'ida ba.
Inuwa ya nuna rashin mahimmancin aikin gina titin “Eastern By-Pass”, bisa la’akari da maƙudan kuɗaɗen da aka ware masa, yana mai cewa mafi yawan kananan hukumomin jihar Katsina ba za su ci gaiyarsa ba.
Bugu da ƙari, ya kuma soki yadda ake bai wa ƴan majalisar dokokin jihar kwangilolin aikace-aikacen gwamnati, inda ya yi kira da a ƙara sanya ido domin ganin gudanar da ayyuka yadda ya kamata domin amfanin al’umma.