Tsaron Makarantu: Gwamnatin Kano na shirin daukar masu gadi 17, 600

Tsaron Makarantu: Gwamnatin Kano na shirin daukar masu gadi 17, 600

Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta kammala shirye-shiryen daukar ma’aikata 17,600 na masu tsaron makarantu da kuma mafarauta na gida domin tabbatar da tsaro ga makarantun gwamnati a kananan hukumomi 44 na jihar.

Kwamishinan Ilimi, Alhaji Umar Doguwa ne ya bayyana hakan a yau Juma’a a Kano lokacin da ya karbi bakuncin mambobin zartarwa na kungiyar tsofaffin daliban makarantar Rumfa, ajin ’94, waɗanda suka ziyarce shi.

A cewarsa, samar da tsaro zai taimaka matuka wajen kare yara daga barazanar iri-iri. Doguwa ya bayyana cewa, domin ilimi ya ci gaba, akwai bukatar hadin gwiwa tsakanin gwamnati, jama’a da kungiyoyin da ba na gwamnati ba domin magance matsalolin da ke tattare da bangaren ilimi.

Kwamishinan wanda ya samu wakilcin babbar sakatariyar  ta ma’aikatar, Hajiya Kubra Imam, ta tabbatar da shirye-shiryen ma’aikatar na aiki tare da kungiyoyin tsofaffin dalibai a fadin jihar domin inganta darajar ilimi.

Kwamishinan ya ce, aniyar gwamnatin kwanan nan na ayyana dokar ta baci a bangaren ilimi wata shaida ce ta gwamnan jihar, Abba Kabir-Yusuf, na neman magance matsalolin ilimi.

Daily Nigerian Hausa
Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org