Wani Magoyin bayan Arsenal ya kashe magoyin bayan Man United saboda murnar cin ƙwallo da Mo Salah yayi.
Muhawarar da ta shafi kwallon Kafa ta ɗauki mummunan yanayi a wata cibiyar kasuwanci ta Kyobgombe da ke yammacin Uganda, yayin da Benjamin Okello mai shekaru 22 ya rasa ransa sakamakon takaddama da wani mai goyon bayan Arsenal a ranar Lahadi, 27 ga watan Oktoba.
Rikicin ya barke ne saboda murna da tsokanar da magoyin bayan Man United ɗin yayi bayan da Arsenal ta tashi 2-2 da Liverpool a filin wasa na Emirates, kamar yadda jaridar Daily Monitor ta Uganda ta ruwaito.
Lokacin da Mohammed Salah ya farke ƙwallo ta biyu a ragar Arsenal cikin mintin karshe a filin wasa na Emirates, mai goyon bayan Manchester United Benjamin Okello yayi murna, inda ya jefa gugguru a kan mai goyon bayan Arsenal duk a lokacin da yake murnar.
Hakan ɗin da yayi ya ƙara ta’azzara lamarin, kuma bayan an kammala wasan ne su biyun suka yi taho-mu-gama, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar Benjamin Okello, bayan da magoyin bayan Arsenal ɗin mai suna Onan ya buge shi da sanda.
Shugaban karamar hukumar Kaharo, Mista Edmond Tumwesigye ya tabbatar da faruwar lamarin, wanda ya bayyana samun labarin faɗan da aka yi da safiyar Litinin.
"Na samu bayanai, wasu mutane biyu sun yi taƙaddama a daren Lahadi a gidan kallon kwallo na wata cibiyar kasuwanci ta Kyobugombe, inda aka garzaya da wanda aka raunata zuwa Cibiyar Kiwon Lafiya ta Bukinda domin yi masa magani, wanda daga bisani ya rasu.” Inji shi.
Shaidu sun bayyana cewa arangamar ta fara ne a wani gidan kallon ƙwallo na yankin, inda magoya bayan kungiyoyin kwallon kafa kan taru don kallon wasannin ƙungiyoyin su.
Daga Lukman Aliyu Iyatawa