Wasu Ƴan'uwa Biyu sun kashe wata Makwabciyarsu bisa zargin Maita
A wani mummunan lamari da ya faru, an kama wasu ƴan uwa biyu Maza bisa zargin kashe wata makwabciyarsu wadda suka zarga da Maita.
Lamarin ya faru ne a kauyen Kashin Dila Fulani da ke karamar hukumar Malam-Madori a Jihar Jigawa, lamarin da ya sa mazauna garin shiga cikin firgici da alhini.
A cewar rahotannin ƴan Sanda, Matasan ƴan’uwan sun haɗa baki ne suka kai wa marigayiyar hari, inda suka raunata ta da sanduna da wukake, wanda hakan ya yi sanadin mutuwar ta.
Bayanai sun cewa ƴan uwan biyu an ce sun yi zargin wata Hauwa Yusai (Marigayiya) da ke zama a gida na kusa da su da cewa mayya ce kuma tana aikata tsafe-tsafe.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin ga wakilinmu ta wayar tarho, jami’in hulda da jama’a na Rundunar ƴan Sandan Jihar Jigawa, DSP Lawan Shiisu Adam ya shaida wa wakilinmu cewa wadanda ake zargin suna tsare kuma za su fuskanci hukunci nan gaba kaɗan.
DSP Lawan ya bayyana cewa ana kyautata zaton dalilin kisan na da nasaba da zargin Chamfi da kuma bayanan da suka samu ba dai-dai ba dangane da marigayiyar.
Daga Lukman Aliyu Iyatawa