Za mu samar da wuta mai amfani da hasken rana cikin rahusa ga ƴan Nijeriya a shekara mai zuwa – FG

Gwamnatin Tarayya ta ce tana kokarin ganin ta samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana ga daukacin ƴan Najeriya a shekara mai zuwa.

Shugaban Hukumar Makamashi ta Najeriya, Dakta Mustapha Abdullahi ne ya bayyana haka a wata hira da yayi da BBC.

Ya yi nuni da cewa, domin Najeriya ta samu wadatacciyar wutar lantarki kamar yadda take a sauran kasashen da suka ci gaba, kasar na bukatar samar da megawatt 40,000.

Kamar yadda kuka sani, duka ƙarfin wutar lantarkin da muke da shi megawatt 12,000 ne a Najeriya, wanda kuma megawatt 5,000 ne kawai ke kaiwa ga jama’ar ƙasa. Kuma Muna bukatar megawatts 40,000 kafin mu iya samar da wadatacciyar wutar lantarki ga Najeriya kamar dai a sauran kasashen da suka samu gaba.

Amma tuni mun gabatar da wani babban tsarin makamashi na ƙasa don magance kalubalen makamashin ƙasar nan da kuma tabbatar da cewa dukkan ƴan Najeriya sun samu wutar lantarki kuma mai rahusa.

“Za mu kafa wata masana’anta da ke samar da na’urorin samar da hasken rana da batura domin ƴan Nijeriya su samu Lantarki mai amfani da hasken rana kuma a rahusa. Ina tabbatar wa ƴan Nijeriya cewa za mu cimma hakan nan da shekara mai zuwa.”

Daga Lukman Aliyu Iyatawa
Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org