Zaɓen 2027: Dole ne Najeriya ta kaucewa zama ƙasa ƙarƙashin ikon jam’iyya ɗaya – Makinde

Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya buƙaci ƴan Najeriya da su tabbatar da cewa ƙasar nan ba ta shiga tsarin Mulkin jam’iyya ɗaya tilo ba, yayin da zaben 2027 ke gabatowa.

Da yake magana kan jita-jitar da ake ta yadawa game da yiwuwar tsayawarsa Takarar Shugaban ƙasa, Makinde ya yi watsi da rade-radin, yana mai cewa shi da kansa zai bayyana aniyarsa idan ya yanke shawarar yin hakan.

Kamar yadda ya bayyanawa manema labarai a Fashola Agribusiness Hub da ke Oyo, Makinde ya jaddada cewa ayyukan da ya yi a Ofis a matsayin gwamna, ba yayi bane saboda wani buri na Siyasa ba anan gaba.

"Ba mu cimma waɗannan nasarori ba saboda ina da burin neman Shugaban ƙasa. Na isa yanke shawara da kai na, kuma idan ina so in yi wani abu, zan fada. Babu wanda zai iya ƙaƙaba Mani abinda ban yi niyyar ɗauka ba," in ji shi.

Gwamnan ya bayyana mahimmancin tabbatar da dimokuradiyyar jam’iyyu da yawa a Najeriya, yana mai gargaɗi kan illolin da za a iya fuskanta idan ya kasance jam’iyya ɗaya tilo ta mamaye madafun iko a ƙasar nan.

Da yake tsokaci kan hawan sa kan karagar mulki, Makinde ya nuna cewa mutanen Oyo sun zabe shi a 2019 ba tare da goyon bayan wani ubangidan Siyasa ba.

Daga Lukman Aliyu Iyatawa
Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org