Ƴan bindiga sun kashe Manoma 10 su na tsaka da Sallah tare da sace Indiyawa a Niger

 Akalla manoma 10 ciki har da mata daga garuruwan Wayam da Belu-Belu a karamar hukumar Rafi ta jihar Neja ne suka  mutu a hannun 'yan bindiga.

Daily Trust ta rawaito cewa mazauna yankin sun ce an datse kawunan mutane shida daga cikin wadanda aka kashe, kuma 'yan bindigar sun tafi da kawunansu.

Sun kuma bayyana cewa mutane da dama sun ji raunukan harbin bindiga kuma ana jinyar su a wani asibiti da ke Kagara, hedkwatar karamar hukumar Rafi.

Rahoton Daily Trust ya kara da cewa an sace mutane da dama yayin harin wanda ya faru da misalin karfe biyar na safe a ranar Talata, lokacin da wadanda abin ya shafa ke cikin sallar asuba.

Kwamishinan tsaro na cikin gida, Birgediya Janar Bello Abdullahi Mohammed, ya ce gwamnatin jihar ta samu labarin harin.

Ya ce, "Gwamnatin Jihar Neja tana sane da lamarin. An tura dukkan hukumomin tsaro don shawo kan matsalar da kuma hana aukuwar irin haka a nan gaba."

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org