Dangantakar da 'Yan'uwanta Tsakanin Katsinawa da Daurawa.

Dangantaka tsakanin Kasar Katsina da Daura ta samo asali tun lokaci Mai tsawo, tun asalin kafuwar Kasashen Hausa. 

Yawancin Kasashen Hausa kamin Jihadin Shehu Usman Danfodio na Karni na (19) suna karkashin ikon Borno, a wancan Lokacin Kuma suna Kai  haraji na karshen Shekara ga Mai na Borno. Ance duk shekara Kasashen Hausa da suka hada da Kano, Katsina, Zazzau,  Daura da sauransu, suna haduwa a Daura domin su tattauna abubuwan da suka shafi Kasar Hausa.

 Wannan haduwar da suke itace ake cema.    (GANI) maana haduwa, daga wajen wannan haduwar ne, Sarakunan Hausa zasu tattara haraji da sauran kyaututuka Wanda zaa kaima  Mai  din Borno. Wannan ya nuna yawancin Kasashen Hausa sun zauna a karkashin ikon Borno kamin Jihadin Shehu Usman Danfodio na Karni na (19). Wannan yana daya daga cikin Dangantaka ta farko tsakanin Kasar Katsina da Daura.   A wajen wannan Taronne Sarkin Daura yakan Shirya Hawan Gani inda  zaayi  Hawa da Dawakai da sauran abubuwan na Garjiya da sauran al'adu, wannan Hawan shine har yanzu ake cema Hawan Gani, Kuma anan ya samo asli. Daga baya a lokacin da Musulunchi yayi karfi sosai sai Sallar Gani ta canza salo, ta koma ana gudanar da ita a watan   Mauludin Nabiyi Sallalahu Alaihi Wassalam, Wanda akeyinta a ranar 12 ga watan Rabial Awwal. Har ya zuwa yanzu Zauren Gani Yana nan a Garin Daura, Wanda Sarakunan Hausa suke Taro a wancan Lokacin. Har ya zuwa yanzu jamaaa da dama daga Katsina suna zuwa Daura don taron Sallar Gani. 
2. Haka kuma a lokacin mulkin Turawa, Daura ta Fara Zama a karkashin  Lardin Kano ( Kano Province). Acikin shekarar 1934 ne  Turawan mulkin Mallaka suka kirkiri Lardin Katsina( Katsina Province). Sai  aka rabo Daura daga Kano ta dawo karkashin Lardin Katsina, wannan ya Kara babbar dangantaka tsakanin Kasar Katsina da Daura. 

3. Ta fannin Ilimin Boko. An bude Katsina Training College acikin shekarar 1922. An samu Dalibai da daman gaske wadanda suka halarci Katsina College a wancan lokacin, daga cikin su akwai 1. Alhaji Muhammad Bashar, Sarkin Daura. Da sauransu. 

  Hakanan Kuma Shugaban Kasar Nigeria Gen. Muhammadu Buhari yayi karatu a Katsina Middle School wadda  makarantar ce ta koma Dikko College a halin yanzu. 

4. Hakanan Kuma Sarkin Daura na yanzu Alhaji Dr. Umar Farouk Umar yaba Katsina da dama Sarautar Kasar Hausa. Daga cikin su akwai. 1. Alhaji Ibrahim Ahmadu Kumasi( An nadashi Garkuwan Hausa a Daura)
  2. Honourably Justice Ummaru Abdullahi( An nadashi Walin Hausa a Daura). 3. Barrister Ibrahim Shehu Shema( An nadashi Sarkin Yakin Kasar Hausa). 4. Alhaji Aminu  Bello Masari( An nadashi Mutawallen Kasar Hausa). 5. Alhaji Kabir Yau Yamel ( An nadashi Sarkin Aikin Kasar Hausa da sauransu. Wannan ya Kara dangantaka Mai karfi tsakanin Mutanen Katsina da Daura. Kuma har ya zuwa yanzu yasancin su suna haduwa Daura wajen Sallar Gani a Kara sadar da zumunci. 

Alh. Musa Gambo Kofar soro.
Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org