DARA TA CI GIDA: Mai maganin gargajiya a Abuja ya raunata kansa yayin gwajin maganin bindiga

 Wani mai maganin gargajiya mai suna Ismail Usman ya samu raunin harbin bindiga yayin da yake gwada laya mai kare harbi a unguwar Kuchibiyi, karamar hukumar Bwari, a Birnin Tarayya, Abuja.

Wani mazaunin Kuchibiyi, Samson Ayuba, ya ce lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, lokacin da mutumin, a kokarinsa na gwada tasirin layarsa mai kare harbi, ya harbi kansa a ciki.

Ya bayyana cewa mai maganin ya yanke jiki ya fadi nan take, sannan wasu maƙwabta suka yi gaggawar daukar sa zuwa asibiti.

“Mutumin bokane, yana hada magunguna da layoyi na gargajiya. A ranar Alhamis, ya yi kokarin gwada bindiga a kan kansa bayan ya sanya laya mai kare harbi, amma layan ya kasa kare shi,” in ji shi.

Yayin tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun rundunar 'yansandan FCT, SP Adeh Josephine, ta ce wanda abin ya faru da shi ya yi amfani da bindigar gargajiya ya harbi kansa a ciki.

Ta ce jami'an 'yansanda daga sashen Byazhin sun yi gaggawar kai dauki inda suka tarar da wanda abin ya shafa cikin mawuyacin hali.

Ta ce bayan kai shi asibiti, ƴansanda sun bincika dakin mutumin inda su ka samu bindiga kirar gida da kuma layoyi daguraye. 

Daily Nigeria Hausa.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org