Dokar haraji: Gwamnan Kano ya zauna da yan majalisar wakilai na Kano
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jagoranci zama na musamman tare da wasu daga cikin yan majalisar wakilai ta kasa da suka fito daga jihar Kano a daren ranar Asabar.
Gwamnan wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, ya tattauna dasu ne akan batun kudirin dokar haraji da Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu take neman majalisun tarayya su amince mata.
Rahotanni na nuni da cewa, Gwamnatin jihar Kano tare da yan majalisar, basu gamsu da kudirin dokar ba, wacce masana ke ganin zata haifar da matsaloli da dama ta fuskar mulkin al'umma, musamman a Arewacin Nigeria.