Fada ya barke tsakanin Dalibai na makarantun sakadari har wasu sun ji raunuka.

 Akwai Dalibai da dama da suka jikkata yayin wani rikici tsakanin Makarantun Sakandare guda 2

Dalibai da dama ne su ka  ji rauni bayan rikici ya barke tsakanin makarantun sakandare a Ilọrin, babban birnin Jihar Kwara.

Channels TV ta rawaito cewa rikicin, wanda ya faru a ranar Litinin, ya jikkata sama da ɗalibai 10.

Wani ganau ya ce rikicin ya fara ne kusan ƙarfe 11:00 na safe, lokacin da wasu ɗalibai daga Government High School suka yi arangama da ɗalibai daga Government Day Secondary School, duk a Adeta, saboda wata rashin jituwa da ta faru a baya.

“Fiye da ɗalibai goma sun ji rauni a wannan rikici da ya jefa yankin cikin rudani. Batun ya fara kusan makonni biyu da suka gabata kuma ya kai ga wannan hali wanda ake zaton ramuwar gayya ce,” cewar majiyar.

Wasu sun danganta wannan lamarin da kungiyoyin asiri da kuma neman iko tsakanin ɗaliban.

Da aka tuntube shi, Sakataren Yaɗa Labarai na ma’aikatar ilimi, Peter Amogbonjaye, ya ce ana shirin fitar da sanarwa kan lamarin.

Kakakin ‘yansandan jihar, Toun Ejire-Adeyemi (DSP), ta tabbatar da faruwar lamarin, tana mai cewa an kama wasu daga cikin waɗanda ake zargi cikin rukuni yayin da ‘yansanda suka yi gaggawar kai ɗauki yayin rikicin.

Ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike don gano musabbabin rikicin.

Sahara Reportes Hausa

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org