Gwamnatin Jihar Katsina ta Bayar da Kyautar Naira Miliyan Ɗaya da Kuma Aiki ga Ƴar Asalin Jihar Katsina da Tazo na Biyu a Gasar Hikayata ta BBC Hausa
A ranar Laraba 27 ga watan Nuwamba 2024, Gwamnan jihar Katsina ya samu wakilcin shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar katsina Hon. Jabiru Abdullahi Tsauri (Lamiɗon Katsina) a wajen bayar da Kyauta ga wanda sukayi nasara a gasar Hikayata ta BBC Hausa a birnin tarayya Abuja.
Gasar Hikayata wata gasa ce da jaridar BBC Hausa ke shirya wa duk shekara ga marubuta masu taso wa, bayan tantance labaran sai a fitar da jerin mutum uku na farko wanda sukayi nasarar lashe gasar.
A gasar ta bana akwai yar asalin ƙaramar hukumar Mashi daga jihar Katsina Amrah Auwal Mashi, da tayi nasarar zuwa mataki na biyu a gasar.
Da yake magana shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar Katsina Hon. Jabiru Abdullahi Tsauri, a madadin gwamnan jihar Katsina, ya nuna jin dadin shi akan shirin Hikayata musamman a wannan karo da aka samu yar asalin jihar Katsina a cikin wanda suka yi nasara a gasar.
Ya ƙara da cewa gwamnan jihar Katsina bai samu halartar taron ba sabo da dalili irin na aikin ofis amma yana ma ɗaukacin mahalarta taron da kuma wanda suka shiga gasar fatan alkhairi.
Ya cigaba da cewa gwamnan ya bada saƙo ga wanda suka shiga gasar domin Ƙarfafa masu guiwa, wanda yace dukkanin wanda suka shiga amma basu samu nasarar zuwa na ɗaya zuwa na Uku ba ya basu kyautar Naira ₦ 250,000, ga kowacce, ta Uku da ta ɗaya kuma ya basu Naira ₦ 500,000 kowace daga cikin su.
Tamu kuma yar asalin jihar Katsina Amrah Auwal Mashi, ya bata Naira Miliyan ɗaya (₦ 1,000,000), a binciken kuma da yayi ya gano cewa tayi karatu ya bata aiki kai tsaye a gwamnatin jihar Katsina.
Daga ƙarshe Lamiɗon Katsina ya jagoranci miƙa lambar yabo ga wasu daga cikin wanda suka yi nasarar.
Shugaban ma'aikatan ya samu rakiyar sakataren gwamnan Hon. Abdullahi Aliyu Turaji.