Gwamnonin PDP Sun Nemi Tinubu Ya Sake Duba Tsare-Tsaren Tattalin Arzikinsa
A cewar gwamnonin, sake fasalin wadannan tsare-tsare zai inganta jin dadin al'umma da walwalarsu.
Kwamitin Gwamnonin jam’iyyar PDP ya nuna damuwarsa kan matsalolin tattalin arziki da ake fuskanta sakamakon manufofin gwamnatin tarayya karkashin jam’iyyar APC. Sun bukaci shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, da ya sake nazari kan tsare-tsaren tattalin arzikin kasa da manufofin kudin gwamnati.
A cewar su, wannan sauyin zai taimaka wajen inganta walwala da jin dadin al’ummar Najeriya.
Wannan bukatar ta kasance daya daga cikin matsayar da kwamitin ya cimma yayin taronsu da aka gudanar a Jos, jihar Filato.
“Kwamitin na jimamin wahalhalun tattalin arziki da ‘yan Najeriya ke fama da su, sakamakon manufofin da gwamnatin tarayya karkashin jam’iyyar APC ta aiwatar,” in ji shugaban kwamitin, Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, bayan taron.