Hukumar Hisbah za ta samar da Tiya (kwanon awo) na musamman ga Ma'aunan hatsi.

 Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina ta jaddada kudirin ta na samar da Tiya ta musamman ga ƴan kasuwar awon hatsi a faɗin Jihar Katsina.

Shugaban Hukumar Malam Aminu Usman (Abu Ammar) ne ya bayyana hakan a lokacin da yake jawabi a wani shirin gidan rediyo na Jihar.

Abu Ammar yace tun bayan kafa hukumar da Gwamnan Jihar Katsina yayi, sun gudanar da ayyuka da suka shafi inganta ɗa'a da kyawawan halayen al'umma, wanda a cewar sa hakan yana rage fushin Allah ga al'umma.

Ya ƙara da cewa, Allah maɗaukakin Sarki yayi jan kunne ga masu tauye Awo, amma abin takaici wannan al'ada ta zama ruwan dare a tsakanin ƴan kasuwa.

Haka kuma ya bada tabbacin cewa nan ba da daɗewa tare da amincewar gwamnan jihar Katsina, hukumar za ta samar da wannan Tiya, kuma ya zama wajibi ga dukkan Ma'auna da su mallake ta tayin saye ko siyar daMa'auna

Daga Lukman Aliyu Iyatawa

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org