Inshallah Shekara Mai Zuwa Za a yi Maulidin Annabi S.A.W da ya dace da 1,500 Da Haihuwa, Ya Kamata Maulidin Baɗi Ya Zama Na Musamman – Sheikh Mai Diwani
Ɗaya daga cikin malaman musulunci, Sheikh Isma’ila Umar Almadda da aka fi sani da Mai Diwani, ya yi kira ga al’ummar musulmi cewa kowa ya yi shiri na musamman a kan gudanar da Maulidin Annabi (SAW) a baɗi idan Allah ya kai mu, saboda a shekarar ce Annabi Muhammadu yake cika shekara 1,500 da haihuwa a duniya.
Ya fadi hakan ne a yayin da yake gabatar da karatu a wurin wani Maulidi da ya gudana a Unguwar Gyaɗi-gyaɗi da ke Kano a yau Lahadi wanda iyalan gidan Alhaji Baballe Ila suka
Sheikh Mai Diwani ya yi bayanin cewa, “Muna kira ga ɗaukacin al’ummar Musulmi kowa ya yi tanadi na musamman kar ya bari a bar shi a baya a baɗi idan Allah ya kai mu. Domin maulidin da za a yi na baɗi shi ne zai zama Manzon Allah (SAW) ya cika shekaru 1,500 da haihuwa.
“Yadda abin yake shi ne, idan ka ɗauki shekarun haihuwar Manzon Allah (SAW) 40 kafin a fara aiko masa da manzanci ka haɗa da shekarun da ya yi a Makkah guda 13 bayan fara saukar da manzanci zai ba ka shekaru 53. To, idan ka haɗa shekaru 53 da shekarar Hijira 1446 a bana, lissafin zai ba ka cewa bana Manzon Allah (SAW) ya cika shekaru 1499 da haihuwa. A baɗi kuma zai zama Manzon Allah (SAW) ya cika shekaru 1,500 da haihuwa kenan.” In ji Sheikh Mai Diwani.
Ya kuma yi kira ga ɗaukacin musulmi kowa ya yi ƙoƙari kar a bar shi a baya wajen yin murnar ganin lokacin da Manzon Allah (SAW) zai cika shekaru 1,500 a duniya a baɗi.
Ya ƙara da cewa, “Hatta waɗanda ba su yin maulidi ya kamata a baɗi su yi kokari su yi wani abu ko yaya kar a bar su a baya, saboda yanzu idan Allah ya ja da rayuwarmu muka ga na baɗi lokacin da Manzon Allah zai cika shekara 1,500 da haihuwa, to zai yi wahala mu ga lokacin da zai cika shekara 2,000 kuma. Domin da wahala a samu wani daga cikin mutanen da ke rayuwa a doron ƙasa yanzu ya ƙara wasu shekaru 500 a raye.”
Ya kuma ba da misali da cewa lokacin da Annabi Isah (AS) ya cika shekaru 2,000 da haihuwa an ga yadda duk duniya ta ɗauki murna, “to mu ma ya kamata Musulmi mu girgiza duniya da bukukuwa na murnar mu ma Annabinmu (SAW) ya cika shekaru 1,500 a duniya. Wannan babban alheri ne da tarihi a rayuwarmu.” in ji Sheikh Mai Diwani.
#Aminiya