Kamfanin BUA ya sanar da samun cinikin naira triliyan 1.07 a wata tara

Kamfanin BUA Foods Plc ya fitar da sakamakon cinikin da ya yi a wata tara da suka gabata, wanda ya ƙare zuwa watan Satumban 2024, inda ya sanar da samun cinikin naira triliyan 1.07 a wata tara.


Wannan na nufin samun cinikin kashi 104, wanda ƙari ne a kan naira biliyan 524.42 da kamfanin ya sanar a irin wannan lokacin a bara, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Kasuwancin sukari ne ya taimakawa kamfanin wajen samun wannan nasara, inda aka samu ƙarin cinikin kashin 73, da ƙarin cinikin kashi 160 a fulawa, da kuma ƙarin cinikin kashi 131 a taliya.

Da yake jawabi a game da sakamakon, manajan daraktan BUA Foods, Dr Ayodele Abioye ya ce, "muna farin cikin samun wannan nasarar, wanda ke nuna yadda tsare-tsarenmu suke aiki, duk da matsalolin da harkokin kasuwanci ke ciki," in ji shi.

Ya ƙara da cewa ciniki ya ƙaru da kashi 104, sannan riba ya ƙaru naira biliyan 333.8 ba ƙaramin nasara ba ne.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org