Kamfanin Mai Na Ƙasa NNPC Zai Ƙara Yawan Man Da Yake Samar Wa Da Ganga Dubu 100,000
Ministan albarkatun mai na ƙasa, Sanata Heine ken Lokpobiri, shi ne ya sanar da hakan a shafinsa na X, wanda aka fi sani da (Twitter) bayan da ministan ya ziyarci wajen aikin da kamfanin ke yi a Jihar Bayelsa domin ƙara yawan man da ake samar wa.
A cewar ministan, aikin yana samun cigaba sosai, "na yaba da yadda na ga aikin na tafiya, a yanzu haka ma adadin man da ake samarwa ya ƙaru da ganga 60,000 inda muke da ƙudirin kai wa ganga 100,000. Mun himmatu kan cimma wannan ƙudirin". In ji shi.
Ministan ya cigaba da cewa suna wannan ƙoƙari ne domin ƙara yawan man da suke samar wa a ƙasa saboda a samu wadatar man tayadda za a daina shiga matsalar ƙarancinsa.