Kudirorin sabuwar dokar haraji ya tsallake karatu na biyu a majalisar dattawa
Kudirorin nan guda huɗu na gyaran dokar haraji da ake ta cece-kuce akan su, da shugaba Bola Tinubu ya miƙa sun tsallake karatu na biyu a majalisar dattawa.
Hakan ya faru ne bayan da jagoran majalisar, Sanata Opeyemi Bamidele (APC, Ekiti ta Tsakiya) ya gabatar da kudirin, wanda ya haifar da muhawara a majalisar a zaman ta na yau Alhamis.
Daga bisani kuma sai kudirorin su ka tsallake karatu na biyu.
~ Daily Nigerian Hausa