Kuskuren da muka yi a Zaɓen Edo ba zai maimaitu ba a zaɓen Ondo - INEC
Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, a ranar Litinin ya tabbatar da cewa zaɓen Gwamnan Jihar Ondo da za a yi a ranar 16 ga watan Nuwamba, zai fi na Jihar Edo da aka gudanar inganci da sahihanci.
A cewar Shugaban INEC, kura-kuren da suka fuskanta a zaɓen Edo za a magance su a zaɓen Ondo.
Yakubu wanda ya je Jihar Ondo domin duba yanayin shirye-shiryen gudanar da zaɓe mai zuwa, ya bayyana cewa hukumar Zaɓen ta shiryawa zaɓen tsaf.
Shugaban na INEC ya ci gaba da cewa hukumar zaɓen za ta yi taro da masu ruwa da tsaki gabanin zaben, inda ya ƙara da cewa za a yi gwajin tantance masu kaɗa kuri’a a kananan hukumomi shida na Jihar.
Yakubu, wanda ya ci gaba da bayyana cewa ƴan Siyasa a Jihar za su sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya, ya ce “Mun samu rahotanni masu inganci daga ofishinmu na Akure, amma kuma mun yanke shawarar zuwa ne domin tantance shirye-shiryen.
“Don haka, mun zo nan ne don mu duba abin da ke faruwa da kuma kyakkyawan aiki da ofishin Jihar ya yi. Za mu gana da masu ruwa da tsaki da suka haɗa da jam’iyyun siyasa, da kungiyoyin farar hula, da kafafen yaɗa labarai, da hukumomin tsaro, sannan kuma za mu gana da ma’aikatanmu domin tantance shirye-shiryenmu. Za mu kasance a nan na ƴan kwanaki.
Mun koyi darussa da dama ba kawai daga zaben da ya gabata ba har ma da wasu zabukan na baya. Ainihin ƙalubalen da muka fuskanta guda biyu ne, wato dabarun gudanar da zabe, da kuma gabatar da sakamakon zaɓe, sai ya tabbatar wa masu kaɗa kuri’a a Jihar Ondo cewa za su ɗauki mataki a waɗannan bangarori biyun.
Daga Lukman Aliyu Iyatawa