Lokaci Yayi Da Ya Kamata Atiku Ya Daina Ɓata Kuɗinsa A Kan Abin Da Ba Zai Samu Ba, Mąrtàniɲ Fadar Shugaban Ƙasa
A wani mārtaɲi da fadar shugaban ƙasa ta fitar ga tsohon mataimakin shugaban ƙasar, Atiku Abubakar kan maganganun da yayi game da cire tallafin man fetur da cin hanci da rashawa, fadar shugaban ƙasar ta bayyana cewa tun bayan da Atiku ya faɗi zaɓen 2023 yake ta ƙoƙarin ɓata shugaba Tinubu da sanyaya masa gwiwa a madadin ya ji da matsalar da am'iyyarsu ta PDP take ciki.
A rahoton da Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta samu, fadar shugaban ƙasa ta bakin mai taimakawa shugaban ƙasar kan yaɗa labarai, mista Bayo Onanuga, Atiku yana hassada ne kawai da shugaba Tinubu saboda ya samu nasarar shiga ofishin da yake fafutukar shiga tsawon karo shida amma bai dace ba. Sannan kuma yana jin haushin gyaran da shugaba Tinubu yake yi wa ƙasa wanda su sun kasa yi a cikin shekaru 16 da suka yi suna mulki a baya.
Sannan kuma, hasashen Atiku kan tattalin arziƙi ya ma nuna ƙarara cewa bai fahimci haƙiƙanin yadda Najeriya take ba. Kuma ba su iya kawo kawo wani gyara a fannin man fetur ba a lokacin da suke mulki. Dan haka tattalin arziƙin Najeriya yana buƙatar ɗaukan matakai na gaggawa masu alfanu. Kuma Wajibi ne ga shugaba ya shirya magance duk wani ƙalubale tun daga ranar farko, kamar dai yadda shugaba Tinubu yayi.
Daɗi da ƙari, mąrtániɲ na fadar shugaban ƙasa ya cigaba da cewa Muna jiran Atiku ya fito ya yaba abin da gwamnatin Tinubu ta yi na samar da bunƙasar yawan kuɗaɗen shiga na cikin gida batare da la'akari da man fetur ba. Da kuma mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000 da 85,000 da ta amince ga ma'aikata.
Sannan kuma gwamnatin Obasanjo da Atiku ce ta ki ba wa ƴan kasuwa damar zuba jarin Dala Miliyan 160 da Dala Miliyan 102 a matatun mai na Fatakol da Kaduna a shekarar 2007 wanda kuma daga baya matatun suka durƙushe.
Haka zalika, Atiku ne ya jagoranci saida wa ɗaiɗaikun mutane kadarorin gwamnati waɗanda yanzu haka duk sun durƙushe.
"Abin mamaki ne ma ace mutumin da yake cikin zarge-zargen badaƙalar cin hanci da rashawa, matarsa take cikin zargin, sannan aka ɗaure abokin kasuwancinsa William Jeffferson na tsawon shekaru 13, amma wai ya fito yana magana a kan cin hanci ?". Fadar ta ce.
Fadar shugaban ƙasar ta ƙara da cewa "Tun 1978 Najeriya take cire tallafin man fetur, kuma an ƙara farashin mai sau 22 daga 1978 zuwa 2020. Kamata yayi Atiku ya ma yabawa ƙoƙarin shugaba Tinubu na farfaɗowa gami da sabuntawa da kyautata tattalin arziƙin ƙasa da yake yi ba wai adawa ta rufe masa Ido ba domin shi ma ya riga ya san cewa cire tallafin man fetur gaba ɗaya abu ne da ya zama wajibi a yi shi".
Sannan kuma, bayan cire tallafin man fetur ɗin gwamnati ta ɗauki matakan rage wa ƴan ƙasa raɗaɗi ta hanyar raba musu tallafin kayan abinci da kuɗaɗe kaitsaye ta cikin asusun ajiyarsu na banki inda sama da ƴan Najeriya mutum Miliyan 20 suka amfana. Haka kuma, gwamnatin ta fito da tsare-tsare daban-daban na gina ƙasa kamar shirin ba wa ɗaliban manyan makarantun gaba da sakandire tallafin bashi (Student Loan) da tsarin motoci masu amfani da iskar gas ta CNG tun a watanni 12 na farko.