Ma'aikatar harkokin kashen ketare ta Qatar ta ce sanar da janyewa daga matsayinta na mai sasantawa a tsakanin Isra'ila da Hamas.
Qatar wacce ta jima tana tattaunawa da shugabannin kungiyar Hamas da na Isra'ila a kokarinta na kawo karshen yakin da ake yi a Gaza, ta ce bangarorin biyu ba da gaske suke yi ba na kawo karshen yakin.
Don haka ta ce ci gaba da yin zaman tattaunawar tamkar ɓata lokaci ne da kuma yaudarar kai saboda jagororin biyu ba da gaske suke yi ba wajen ganin an kawo ƙarshen wannan taƙaddama.