Matatar mai ta Dangote ta sanar da rage farashin man fetur ga ‘yan kasuwa.
Dangote ya rage farashin man fetur
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Anthony Chiejina, Babban Jami’in Sadarwa na Rukunin Kamfanin Dangote, ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.
Ya ce farashin fetur ya sauka daga N990 kowace lita zuwa N970 kowace lita, domin nuna godiya ga al’ummar Najeriya.
“Yayinda shekarar ke gab da ƙarewa, wannan hanya ce da muke godiya ga mutanen Najeriya masu kwazo bisa goyon bayansu wajen ganin mafarkin samar da wannan matatar ya zama gaskiya. Haka kuma, muna godiya ga gwamnati bisa goyon bayan da suka bayar don inganta harkokin kasuwanci na cikin gida domin amfanin kowa da kowa,” in ji shi.