Mun yabawa Shugaba Tinubu bisa yadda ya karbi shawararmu ya saki yara yan zanga-zanga ba tare da sharadi ba -inji Shugaban JIBWIS Bala Lau
Bala Lau ya ce sun shiga sun fita domin ganin an saki yaran, kuma yana fata matasa za su riƙa jin shawara a duk lokacinda aka ce kada suyi wani abu
A karshe Shugaban Izalar ya kuma yi kira ga yan Najeriya su tashi tsaye wajen yiwa Gwamnatin Najeriya addu'a Allah ya sanya albarka a mulkinsu ya kawo karshen matsalolin da kasar ke fuskanta.
"Muna fata matasa za su rungumi karatu da sana'a, Gwamnati ita kuma ta samar da ayyukan yi ta yadda ko an kirawo matasa suyi abunda ya saɓawa doka ba za su amsa kiran ba saboda ayyukan gabansu" inji Lau