Naira biliyan 8.8 gwamnatin taraiya ta kashe wajen gyaran wutar lantarki da aka riƙa lalata wa a 2024 – TCN
Sule Abdulaziz, Manajan Darakta na Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Najeriya (TCN), ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya ta kashe kimanin Naira biliyan 8.8 wajen gyaran turakun wutar lantarki da aka lalata a sassa daban-daban na kasar.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin Mr. Abdulaziz, wanda aka wakilta ta hannun Mr. Olugbenga Ajiboye, Daraktan Gudanarwa na Mai Samar da Ayyukan Rarraba Wutar Lantarki (TSO), a yayin taron kwata-kwata na Rukunin Aikin Bangaren Wutar Lantarki da aka gudanar ranar Talata a birnin Abuja.
Ya bayyana cewa an lalata jimillar Turaku 128 daga watan Janairu 13, 2024, zuwa yanzu, ta hannun masu lalata kayayyakin gwamnati da ‘yan bindiga. Ya koka kan yadda ake ci gaba da lalata muhimman kayayyakin more rayuwa da kuma rashin tasirin matakan shari’a kan masu aikata laifin da aka kama.
Abdulaziz ya kuma bayyana kalubalen da TCN ke fuskanta wajen dawo da muhimman layukan wutar lantarki, kamar layukan Shiroro-Mando-Kaduna. Ya kara da cewa kamfanin ya tilasta daukar sojoji don rakiyar kwangiloli saboda matsalolin tsaro.