Tsare Kananan Yara: Tinubu ya bada umarnin sakin Yaran da Rundunar ƴan Sanda ta kama
Bayan yin kira ga Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya gaggauta sakin yara 76 da Rundunar ƴan Sandan Najeriya ta gurfanar a gaban kuliya saboda shiga zanga-zangar adawa da gwamnati da aka gudanar a ƙasar nan.
Dimokuradiyya TV ta ruwaito a baya cewa wani karamin yaro wanda yana cikin yara 76 da aka gurfanar ranar Juma’a a wata babbar kotun Tarayya da ke Abuja saboda shiga zanga-zangar EndBadGovernance da aka gudanar a baya-bayan nan, ya yanke jiki ya faɗi ana gab da soma shari’arsu.
Yaron wanda bai wuce shekaru 15 ba, ya faɗi kasa ne a lokacin da ake shirin karanto tuhumar da ake akan su a gaban mai shari’a Obiora Egwuatu.
Lamarin dai ya tilasta wa alkalin ya dakatar da shari’ar ba tare da bata lokaci ba inda ya koma Ofishin sa.
An garzaya da yaron zuwa asibitin cikin kotun yayin da waɗanda ake tuhumarsa a tare wanda mafi yawancinsu yara ne ƙanana sun ɗimauta a sabili da faruwar lamarin.
Ɗaya daga cikin lauyoyin da ke kare waɗanda ake karar, Mista Deji Adeyanju ya bayyana a baya cewa yaran sun shafe sama da kwanaki 80 a hannun ƴan Sanda.
Kungiyar masu fafutukar kare hakkin bil’adama, HURIWA, a wata Sanarwa da ta fitar mai ɗauke da sa hannun Ko'odinetanta na ƙasa Emmanuel Onwubiko, ta bayyana cewa, matakin da Rundunar ƴan Sandan Najeriya ta ɗauka bai dace ba akan ƙananan yara haka.
Daga Lukman Aliyu Iyatawa