Wata Sabuwar Dabbarwar Kan Zargin Badakalar Naira Biliyan 110: EFCC Ta Tabbatar Da Dakume Yahaya Bello
Rahoto
Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzƙin Najeriya ta'annati, EFCC, ta ce ta kama tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a yau Talata.
Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzƙin Najeriya ta'annati, EFCC, ta ce ta kama tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, a yau Talata.
Kafin hukumar ta tabbatar da kama shi rahotanni da dama na ambato cewa, tsohon gwamnan wanda ke fuskantar tuhumar almundahana, ya kai kansa ne ofishin hukumar da ke Abuja tare da rakiyar wasu lauyoyinsa.
A wani hoton bidiyo na tashar talabijin ta Channels, kakakin hukumar ta EFCC, Dele Oyewale, ya tabbatar da cewa hukumar tana tsare da tsohon gwamnan na Kogi.
Taƙaddama ta kasance tsakanin EFCC da tsohon gwamnan, bayan da hukumar ta ayyana nemansa a watan Afirilu, bayan ya ƙi amsa gayyatar da ta sha aika masa tare da nuna tirjiya kan duk wani yunƙuri na kama shi, wanda hakan ya sa ya shiga kulli-kurciya da hukumar.