Waye Rabiu Ali ɗan wasa mafi tsufa a gasar NPFL:
An haifi Rabiu Ali a ranar 27 ga Satumba 1980 (Yanzu yana da shekaru 44) a cikin birnin Kano dake Najeriya.
Dan wasan tsakiya ne na Najeriya wanda ke buga wasa a kungiyar Kano Pillars F.C. kulob din dake fafatawa a gasar kwararrun kwallon kafa ta Najeriya Ya koma Kano Pillars a shekarar 2009.
Ya buga wasanni 18 a cikin tawagar kasa inda ya zura kwallaye 5 Shi ne kyaftin din Kano Pillars F.C. Yana daya daga cikin manyan 'yan wasan kungiyar kuma daya daga cikin manyan 'yan wasa a NPFL. Duk masoya kwallon kafa na Kano suna son shi.
● Fagen Wasanni