Yar Majalisar Dokokin Jihar Kaduna Munirat Ta Gabatar Da Kudurin Baiwa Jinsin Mata Kashi 40% Na Mukamai A Hukumomin Gwamnati Da Nade-Nade
Daga Shuaibu Abdullahi
Yar majalisar dokokin jihar Kaduna Mai wakiltar karamar hukumar Lere ta gabas, Honorabul Munirat Tanimu, ta gabatar da kudurin bukatar baiwa jinsin mata kashin 40% cikin 100% na mukamai a hukumomin Gwamnati da sauran nade-nade a Jihar Kaduna.
To sai dai Yar majalisar ta fuskanci tutsu daga Yan'uwanta Yan majalisu, inda suka ki mara mata bayan tabbatar da kudirin, sai dai ta sami kuri'ar Honorabul Henry Mara, shi kadai.
A take Honorabul Munirat Tanimu, ta nuna alhinin ta a fili kan yadda Yan majalisun suka yi mata bore.
Ta ce da akwai Yan majalisu irin ta mata biyu ko uku a zauren majalisar da sun mara mata bayan wajen tabbatuwar kudirin don ya zama doka.
Sai dai daga bisani ta ce kudirin na ta yana da wuyar samun shiga, saboda lamari ne daya danganci baiwa mata mukami Kuma a Arewa.
Munirat Tanimu, ta kasance Yar majalisa daya tilo a zauren majalisar dokokin jihar Kaduna, Kuma ita ce Shugabar masu rinjaye ta majalisar.