Zan zubawa China da Mexico da Canada haraji tun daga ranar da aka rantsar da ni - Trump

 Zababben shugaban Amurka Donald Trump a jiya Litinin ya ce, da zarar ya shiga fadar White House, zai sanya haraji mai yawa akan shigo da kayayyaki daga kasashen Mexico da Canada da kuma karin haraji kan kayayyakin da China ke shigowa da su.

Trump ya fadi hakan a shafinsa na Truth Social, dandalin sada zumunta da ya kafa, cewa zai rattaba hannu kan wata doka ta zartar da hakan a ranar farko da ya hau kan karagar mulki.


"A ranar 20 ga watan Janairu, a matsayin daya daga cikin umarni na na farko na zartarwa, zan sanya hannu kan duk wasu takaddun da su ka wajaba don karɓar harajai daga Mexico da Canada da harajin kashi 25 cikin 100 akan duk kayayyakin da ke shigowa Amurka, da kuma Budaddiyar Iyakoki," in ji Trump.

#Daily Nigeria Hausa 

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org