2027; Ba mu da kwarin gwiwa kan INEC don gudanar da sahihin zaɓe -'Yan Nijeriya
Wasu daga cikin ‘yan Najeriya sun bayyana rashin gamsuwa da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) dangane da yadda ta ke gudanar da shirye-shiryen zabe na shekarar 2027. Sun yi ikirarin cewa hukumar ba ta da kyakkyawan tsarin da zai tabbatar da sahihanci zaben, tare da nuna zarginsu na shirin yin magudi a zaben mai zuwa.
Masu sukar sun yi nuni da cewa matsalolin da suka shafi rashin bin ka’idoji da rashin amfani da fasahohi masu kyau sun haifar da rashin kwarin gwiwa. A cewarsu, gazawar INEC wajen tabbatar da adalci a zabukan baya ya sa ake zargin za a iya samun irin matsalolin nan gaba.
Wata kungiya mai kare hakkin dan Adam ta yi kira ga gwamnatin Najeriya da sauran masu ruwa da tsaki da su tabbatar da cewa INEC ta gyara dukkan matsalolinta kafin babban zaben 2027. Kungiyar ta ce gyara tsarin zabe na iya karfafa dimokuradiyya da zaman lafiya a Najeriya.