A biya Yan NPower kudade su cikin awanni 72 Majalisar wakilan Nijeriya ta bukaci Shugaba Tinubu ya biya matasan da suka yi shirin N-Power hakkokinsu cikin sa'o'i 72
Majalisar wakilan Nijeriya ta bukaci shugaba Bola Tinubu da ya umarci ministan kudi da harkokin tattalin arziki,
Wale Edun, kan ya tabbatar da cewa an bude dukkanin asusun hukumar kula da harkokin bayar da tallafi ta kasa (NSIPA) da aka rufe a baya, cikin sa’o’i 72, domin samun damar gudanar da shirye-shiryen hukumar yadda ya kamata.
Majalisar ta kuma bukaci ministan ya tabbatar an tura kudade ga hukumar ta NSIPA domin biyan bashin alawus-alawus na matasa dubu 395 da 731 da suka yi shirin N-Power a fadin kasar, ba tare da bata lokaci ba.
Kazalika majalisar ta bukaci Ministan jin kai da ayyukan agaji, Nentawe Yilwatda, da ya tabbatar da an magance matsalolin da ke kawo cikas ga duk wani shiri karkashin hukumar ta NSIPA cikin sauki. Kuma akan Lokaci.
Me zaku ce kan hakan?