A Jihar Katsina Yan sanda sun kama ‘Yan Ta’adda Dauke da Kayan Sojoji

Aminu Hassan ɗan shekara 25 da ya fito daga ƙauyen Dundubus a ƙaramar hukumar Ɗanja ya fara zuwa hannu.

Da yake gabatar da waɗanda ake zargi da ta’adancin, jami’in yaɗa labarai na rundunar ‘yan sanda ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya ce sun kama Aminu Hassan ne a ƙaramar hukumar Ɗanmusa ɗauke da kayan sojoji har guda biyu .

Ya ƙara da cewa shi wannan ɗan ta’adda ya maida garuruwan da ke ƙaramar hukumar Ɗanmusa a matsayin wajen da yake aikata ta’adancin sa.

ASP Abubakar Sadiq ya bayyana cewa binciken da ‘yan sanda suka gudanar ya sanya suka ƙara kama wasu mutane uku da Lawal Ahmed ɗan shekara 29 da Ismaila Dalhatu da suka fito daga garin Basawa a ƙaramar hukumar sabon Gari Zaria.

“Sai shafi’u Adamu ɗan shekara 28 daga ƙauyen Ɗanjaba a ƙaramar hukumar Soba a Jihar Kaduna”ASP Sadiq ya faɗi haka.

Ya cigaba da cewa waɗannan yan ta’adda su uku da aka kama, bayan gudanar da bincike an kama su ɗauke da kayan sojoji na mutum 14 da na ɗan sanda gudu ɗaya.

Jami’an yaɗa labarai na yan sanda ya bayyana cewa su waɗannan yan ta’adda da aka kama ana zargin da amfani da kayan sojojin wajan aika ta’adanci.

‘Yan sanda kuma sun kama wani mutum mai suna Mu’azu Yunusa da ke zaune a ƙauyen Danƙo dake garin Tudun Willi a ƙaramar hukumar Kankiya da taimakawa ‘yan ta’adda.

ASP Abubakar Sadiq ya faɗawa manema labarai cewa Mu’azu Yunusa nada hannu wajan sace mata biyu a gidan wata a nan garin Kankiya inda ya buƙaci biyan kuɗin fansa.

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina



‘Haka kuma wanda ake zargin ya taimaka wajen garkuwa da wani abokin sa da Ke zaune a nan garin Kankiya”.ya faɗi haka.


ASP Abubakar Sadiq ya bayyana cewa da zaran ‘yan sanda sun kamala bincike za a gurfanar da su a gaban kuliya.

Next Post Previous Post
No Comment
Add Comment
comment url
sr7themes.eu.org