A Nijeriya Gwamnonin jihohi 36 sun cimma Masltsaya kan kafa ’yan sandan jihohi don nufin shawo kan matsalar tsaro.
Gwamnonin sun cim ma wannan matsaya ne a taron Majalisar Tattalin Arziƙi na Ƙasa wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya jagoranta a Fadar Shugaban Ƙasa ranar Alhamis.
Gwamnonin jihohi 36 sun yi ittifakin kafa ’yan sandan jihohi da nufin shawo kan matsalar tsaro.
Gwamnonin sun cim ma wannan matsaya ne a taron Majalisar Tattalin Arziƙi na Ƙasa wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ya jagoranta a Fadar Shugaban Ƙasa ranar Alhamis.
’Yan sandan jihohi na daga cikin matakan da gwmanati ke tunanin amfani da su domin magance matsalar tsaro a sassan Najeriya.
A taron da Majalisar Tattalin Arziƙi ta Ƙasa ta gudanar a watan Nuwamba, Jihohin Adamawa sa Kebbi da Kwara da Abuja ne kaɗai ba su miƙa rahotonsu kan lamarin ba.
Gobara ta cinye kamfanin shinkafa ƙurmus a Kogi
NAJERIYA A YAU: Yadda ya kamata alaƙa ta kasance tsakanin ’yan sanda da al’umma
Amma bayan zaman na ranar Alhamis Gwamnan Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa yanzu kowace jiha ta mika rahotonta.
Sai dai ya bayyana cewa Sakatariyar Majalisar za ta yi aikin tattara rahotannin da nufin tuntuɓar masu ruwa da tsaki a kan lamarin kafin zama na gaba a watan Janairun 2025.
Ya ce tattaunawar da aka yi a taron ya amince da cewa da buƙatar kafa ’yan sandan jihohi musamman saboda gazawar tsarin jami’an tsaro na ƙasa sannan kowane yanki na da matsalar tsaron da ya keɓance shi.
Ya ce an jinkirta abin zuwa zaman watan Janairu ne domin Sakatariyar Majalisar ta tsara yadda za a tuntuɓi masu ruwa da tsaki kafin daga karshe a aiwatar.